HomeSashen Hausa'Yanbindiga sun kai hari a ƙauyuka 16, sun yi ajalin mutum 5,...

‘Yanbindiga sun kai hari a ƙauyuka 16, sun yi ajalin mutum 5, tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar Zamfara.

-

‘Yanbindigar da suka kai hari a ƙalla garuruwa 16 tsakanin Asabar da Lahadi, a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara, sun yi ajalin mutane 5 tare da yin garkuwa da Mata da dama.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, a ranar Asabar, ‘yanbindigar sun yi awon gaba da mutane 8 ciki har da Dan Isa, Kyatawa, Tudu, Gidan Haruna, da sauransu, inda suka kashe mutum 1 a Gidan Haruna kuma suka sace mata 8.

A ranar Lahadi kuma, sun sake dawowa Kwalau inda suka kashe mutum 4, Abubakar, Murtala, Aminu da Bello tare da raunata wani Ashafa, wanda aka kai asibitin Kaura Namoda.

Rahotan jaridar Daily Trust, ya ce ‘yan sa-kai sun yi musayar wuta da ‘yanbindigar a daren Asabar, lamarin da ya sa suka ja da baya.

Sai dai, da safe sun dawo cikin shiri, inda suka kai farmaki wajen taron ‘yan sa-kai, inda suka kashe 4, suka raunata 1, tare da sace Mata da kwashe kayan Abinci da na gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular