HomeSashen HausaGwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani Ya Sauya Muƙaman wasu Kwamishinoni guda...

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani Ya Sauya Muƙaman wasu Kwamishinoni guda biyu

-

Gwamnan, ya aiwatar da wani ƙaramin sauyi a cikin Majalisar Zartaswarsa ta Jihar, inda ya sauya mukaman wasu manyan kwamishinoni guda biyu domin ƙara kuzarin aikin gwamnati jihar da inganta ayyuka ga al’ummar Jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa, Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Sule Shu’aibu (SAN), an tura shi zuwa Ma’aikatar tsaro da harkokin cikin Gida.

James Kanyip (PhD), wanda ke rike da wannan kujera a da, shi kuma zai maye gurbinsa a matsayin sabon Babban Lauyan Gwamnatin jihar da kuma Kwamishinan Shari’a.

Musa ya bayyana cewa wannan sauyin an yi shi ne domin ƙarfafa aikace-aikacen ma’aikatun ta hanyar amfani da ƙwarewar kowa ne kwamishina.

Gwamna Uba Sani ya umarci waɗannan manyan jami’an biyu da su rungumi sabbin ayyukansu a bisa gaskiya da adalci, inji sanarwar.

Gwamnan ya bayyana cikakken gamsuwar shi da ƙwarewar da kowannen su zai kawo a sabbin maƙaman nasu, yana mai cewa isar da ayyuka mai inganci shi ne ginshiƙin gwamnatin tasa.

Koda yake an bayyana sauyin a matsayin “kaɗan,” masana harkokin siyasa sun ce mukaman da aka sauya na daga cikin mafi muhimmanci da tasiri a jihar ta Kaduna, wato ɓangaren Shari’a dana tsaron cikin, waɗan da sune ke da rawar gani wajen yaki da ’yan bindigar daji, garkuwa da mutane, da kuma gyaran tsarin shari’a a jihar ta Kaduna nan.

Sule Shu’aibu, wanda lauya ne mai daraja ta SAN, ya shahara wajen jagorantar gyare-gyare a cikin tsarin shari’ar jihar Kaduna.

Matsar da shi zuwa Ma’aikatar Tsaro na Cikin gida zai sanya shi a sahun gaba wajen dai daita harkokin tsaro, musamman duba da ƙararrawar hare-haren ’yan bindiga a yankunan karkara da tashin hankali tsakanin al’ummomi.

A daya bangaren kuma, Dr. James Kanyip, masani ne a fannin shari’a da kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gwamna, wanda ke da zurfin ilimi da ƙwarewar gudanarwa da za su taimaka masa a sabon mukaminsa a Ma’aikatar Shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular