HomeSashen HausaƘasar Mali Ta Ƙirƙiri Sabuwar Rundunar Soji Ta Musamman

Ƙasar Mali Ta Ƙirƙiri Sabuwar Rundunar Soji Ta Musamman

-

Ƙasar Mali, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Mulkin Soji, Kanal Assimi Goïta, ta ƙaddamar da wata sabuwar rundunar soji ta musamman mai suna Rapid Intervention Battalion (RIB).

‎Manufar kafa wannan runduna ita ce ƙarfafa ƙarfin aiki da ingancin rundunar Sojojin Mali (FAMa), tare da inganta saurin mayar da martani ga duk wani nau’in barazanar tsaro a fadin kasar.

‎Sabuwar rundunar za ta kasance mai saurin motsi da tsauraran horo, domin tinkarar hare-haren ‘yan ta’adda, rikice-rikicen cikin gida da kuma kare ikon ƙasa da lafiyar al’umma.

‎Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Mali ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro, musamman a yankunan arewa da tsakiyar kasar, inda gwamnati ke ƙoƙarin ƙarfafa ikon ta da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Gobara Ta Tashi A Ofishin Hukumar Karbar Haraji A Abuja

Wata gobara ta tashi a ɗaya daga cikin ofisoshin Hukumar Karɓar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da ke birnin tarayya Abuja, lamarin da ya tayar da...

POCACOV: Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina Ta Kara Zage Dama Wajen Yaki da Laifuka

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Bello Shehu, MNIM, ta shirya wani Maci na wayar da kan jama’anta kan Yaki...

Most Popular