HomeLabaraiShugaban Rundunar Horaswa ta Sojin Sama Ya Kai Ziyara Kainji, Ya Jaddada...

Shugaban Rundunar Horaswa ta Sojin Sama Ya Kai Ziyara Kainji, Ya Jaddada Shirye-shiryen Murƙushe ‘Yan Ta’adda

-

Shugaban rundunar horaswa ta Sojin Sama ta Nijeriya, Air Vice Marshal Esen Paul Efanga, ya kai ziyara sansanin Sojin Sama na Kainji domin duba

‎shirye-shiryen aiki da ƙarfinsu wajen yaƙi da ƴan ta’adda a sassan ƙasar nan.

‎A yayin ziyarar, Efanga ya yabawa jami’ai bisa ƙwazo da jajircewa, tare da nuna gamsuwa da yadda jiragen sama ke gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

‎Ya jaddada cewa Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya na ci gaba da samun rinjaye a sararin samaniya, tare da cikakken shiri na kai farmaki a kowane lokaci.

‎Shugaban rundunar ya kuma tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa Sojin Sama na da cikakken iko da ƙarfin kare martabar ƙasa, inda ya ce ba za a sassauta ba wajen ci gaba da kai hare-hare cikin ƙarfi da daidaito har sai an samu tsaro mai ɗorewa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎An Cafke Wani Mutum Da Zargin Sayar Da Jaririn ‘Yar’ uwarsa Naira Miliyan 2 a Legas

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 30 da haihuwa bisa zargin sayar da jaririn ‘yar uwarsa mai wata daya kacal...

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun damƙa matashiya Walida Abdullahi Ibrahim ga Gwamnan Jihar Jigawa,...

Most Popular