HomeLabaraiMutane 23 Sun Mutu, Sama da 100 Sun Jikkata a Harin Bama-bamai...

Mutane 23 Sun Mutu, Sama da 100 Sun Jikkata a Harin Bama-bamai a Maiduguri

-

‎Aƙalla mutane 23 sun mutu, yayin da mutane 108 suka jikkata sakamakon wasu jerin fashewar bama-bamai da suka auku a daren Litinin.

‎Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta ce hare-haren sun faru ne a wurare masu cunkoso, ciki har da kasuwar Monday Market, ƙofar asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da kuma gadar sama ta Post Office.

A rahoton da Nigerian Post ta samu, ‎Mai magana da yawun rundunar, Nahum Kenneth Daso, ya ce an yi amfani da na’urorin fashewa na IED, yana mai cewa an kai hare-haren ne a lokaci guda a wurare daban-daban.

‎Jami’an tsaron dai sun killace yankunan tare da fara bincike, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci.

‎Kwamishinan ’yan sanda, Naziru Abdulmajid, ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa, tare da tabbatar da ƙara tsaurara matakan tsaro.

‎Hukumomi sun buƙaci al’umma su kasance cikin lura tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎An Cafke Wani Mutum Da Zargin Sayar Da Jaririn ‘Yar’ uwarsa Naira Miliyan 2 a Legas

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 30 da haihuwa bisa zargin sayar da jaririn ‘yar uwarsa mai wata daya kacal...

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun damƙa matashiya Walida Abdullahi Ibrahim ga Gwamnan Jihar Jigawa,...

Most Popular