HomeLabaraiNASA Ta Fitar da Hotunan “Earthset” da Kusufin Rana Daga Duniyar Wata

NASA Ta Fitar da Hotunan “Earthset” da Kusufin Rana Daga Duniyar Wata

-

Hukumar kula da sararin samaniya ta NASA tare da haɗin gwiwar Airbus Space da kuma Canadian Space Agency sun fitar da sabbin hotuna masu ban sha’awa daga shirin Artemis II, inda aka hango abubuwan da ba kasafai mutane ke gani ba daga doron wata.

‎A ranar 6 ga watan Afrilu, 2026, an ɗauki hoton abin da masana ke kira “Earthset”, wato lokacin da duniya ke ɓacewa a sararin samaniya kwatan-kwacin yadda rana ke faduwa a doron ƙasa. Wannan yanayi ya fito ne daga hangen nesa na masu zagaya duniyar wata, inda duniya ke sauka a bayan doron wata.

‎Haka kuma, a ranar 7 ga watan Afrilu, an sake ɗaukar wani abin mamaki inda duniyar wata ta rufe rana gaba ɗaya (totality) — wani nau’in kusufin rana da ake gani daga sararin wata. Wannan dai na nufin wata ya shiga tsakanin rana da mai kallo, lamarin da ya samar da duhu na ɗan lokaci a sararin subuhana.

‎Masana sun ce irin wannan gani yana daga cikin abubuwan da ba kasafai ɗan adam ke samu ba, musamman daga wajen da ba doron ƙasa ba. Shirin Artemis II yana daga cikin manyan tsare-tsaren da ake yi domin sake kai mutane zagayen duniyar wata, kafin a kai ga saukar da mutum a cikinta nan gaba.

‎Rahotanni sun nuna cewa waɗannan hotuna sun ƙara nuna irin cigaban da ake samu a binciken sararin samaniya, tare da bai wa masana damar fahimtar yanayin kusufin rana da motsin duniyoyi daga wani sabon matsayi.

‎Ana sa ran irin waɗannan bayanai za su taimaka wajen ƙara inganta shirye-shiryen bincike da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe a fannin sararin samaniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Wamba Reaffirms Himself as Legitimate ADC Chairman in Katsina

The Chairman of the African Democratic Congress (ADC) in Katsina State, Musa Usman Wamba Funtua, has reaffirmed that he remains the legitimate leader of the...

APC Denies Interference in ADC Crisis, Challenges Allegations

The All Progressives Congress (APC) has challenged the African Democratic Congress (ADC) over its allegations that the ruling party is interfering in its internal crisis. APC’s...

Most Popular