HomeSashen HausaKo Seyi Tinubu Ne Ya Zama Shugaban INEC, APC Za Ta Sha...

Ko Seyi Tinubu Ne Ya Zama Shugaban INEC, APC Za Ta Sha Kaye a 2027 -inji Dalung

-

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa jam’iyyar APC da shugaban ƙasa Bola Tinubu ba za su tsira ba a zaben 2027, ko da kuwa sun dauki matakan da suka fi karfi don su ci zabe.

Hakan na ƙunshe ne a wata hira da aka yi da shi a tashar News Central a ranar Juma’a, Dalung ya ce ko da dukkan gwamnoni 36 na kasa sun sauya sheka zuwa APC, kuma shugaban kasar ya nada dansa, Seyi Tinubu, a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), hakan ba zai hana jam’iyyar faduwa a zabe mai zuwa ba.

“Ko da duk gwamnoni 36 sun koma APC, kuma ya nada Seyi Tinubu shugaban INEC, har da matarsa ta zama shugaban kotun koli, za su sha kaye a 2027,” in ji Dalung.

Haka kuma, Dalung ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa al’umma kasa yaki, inda ya ce talauci, yunwa da rashin adalci sun zama ruwan dare a kasar. Ya kara da cewa Gwamnati ta mayar da cin hanci da rashawa da rashin tausayi tamkar wata doka ce.

“Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fitar da jadawalin yaki ga ‘yan Najeriya. Ta mayar da talauci da yunwa da tsadar rayuwa makamai, sannan ta yayata rashawa da rashin adalci,” in ji Dalung.

Tunda farko, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su mara baya ga sabuwar kawancen siyasa da ke tasowa don kalubalantar gwamnatin mai ci a zaben 2027. “Dama guda da muke da ita ita ce mu hade da wannan sabuwar tafiya domin sake farfado da kasar nan,” ya ce.

Kamar yadda Nigerian Post take bibiyar rahotanni, Dalung, wanda ya taɓa zama mamba a gwamnatin Buhari, ya kasance ɗaya daga cikin masu sukar mulkin APC na yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

NATA Mourns Former President Buhari, Describes Him as a Pillar of National Service

NATA Mourns Former President Buhari, Describes Him as a Pillar of National Service Nigeria Automobile Technicians Association (NATA) Katsina State Council Mourns the Passing of Former...

Katsina NUJ Mourns Former President Muhammadu Buhari, Describes His Death as Monumental Loss

The Katsina State Council of the Nigeria Union of Journalists (NUJ) has expressed deep sorrow over the death of Nigeria’s former President, Muhammadu Buhari, GCFR,...

Most Popular