Shugaban Rundunar Horaswa ta Sojin Sama Ya Kai Ziyara Kainji, Ya Jaddada Shirye-shiryen Murƙushe ‘Yan Ta’adda

Shugaban rundunar horaswa ta Sojin Sama ta Nijeriya, Air Vice Marshal Esen Paul Efanga, ya kai ziyara sansanin Sojin Sama na Kainji domin duba

‎shirye-shiryen aiki da ƙarfinsu wajen yaƙi da ƴan ta’adda a sassan ƙasar nan.

‎A yayin ziyarar, Efanga ya yabawa jami’ai bisa ƙwazo da jajircewa, tare da nuna gamsuwa da yadda jiragen sama ke gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

‎Ya jaddada cewa Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya na ci gaba da samun rinjaye a sararin samaniya, tare da cikakken shiri na kai farmaki a kowane lokaci.

‎Shugaban rundunar ya kuma tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa Sojin Sama na da cikakken iko da ƙarfin kare martabar ƙasa, inda ya ce ba za a sassauta ba wajen ci gaba da kai hare-hare cikin ƙarfi da daidaito har sai an samu tsaro mai ɗorewa.