HomeSashen HausaSule Lamido Na Shirin Shiga Haɗaka Don Kawar Da Tinubu A 2027

Sule Lamido Na Shirin Shiga Haɗaka Don Kawar Da Tinubu A 2027

-

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga kowace haɗakar jam’iyyun siyasa da nufin kawar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki a shekarar 2027 da ke nan gaba.

Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a karshen mako a ɓangaren siyasa.

Nigerian Post ta samu cewa, ya yin da yake sukar gwamnatin Tinubu da zargin gazawa da rashin ƙwarewa, Lamido ya jaddada buƙatar kawar da jam’iyyar mai mulki ta APC daga mulki, wanda ya ce tuni ya fara shirye-shiryen yin hakan.

Fitaccen jigon jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce a shirye yake ya shiga kowace irin haɗaka ce ta jam’iyyu, matuƙar za a kawar da gwamnatin yanzu daga mulki.

A cewar sa shi ɓangare ne na kowace haɗaka da ake shirin ginawa a ƙasar, da nufin kawar da wannan gwamnati marar ƙwarewa, mai kawo rashin tsaro, da ke raba Najeriya tsakanin Arewa da Kudu. Ya ce zai bada kowacce irin gudummawa, domin ganin an cimma manufa tare da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Tinubu Ya Sauya Shugabannin Sojoji, Ya Nada Sabbi Don Ƙarfafa Tsaron Ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sauya manyan shugabannin rundunonin tsaron ƙasar nan domin ƙarfafa tsarin tsaro da inganta tsare-tsaren kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Kamar...

Ma’aikatar Lafiya Tayi Bankwana Da Babban Sakataren Ta, Dr. Ahmed Tijjani Hamza, Bayan Wa’adin Aikinsa Ya Kare A Jihar Katsina

Ma'aikatar Lafiya ta jihar Katsina ta shirya ma Dr. Ahmed Tijjani Hamza, gagarumar liyafa, tare da karramawa, a yayin da yake bankwana da ma'aikatan sashen...

Most Popular