Wata Kotu a Kano, ta yanke wa ɗan Tiktok mai saka rigar mama da wanka akan titi hukuncin shekara ɗaya a gidan gyaran hali.
Kotun Majistiri mai lamba 21 dake zamanta a Gyadi-gyadi, karkashin jagorancin mai sharia Hadiza Muhammad Hassan, ta yanke wa matashinnan Umar Hashim Tsulange da ya kware wajan sanya rigar mama, yana wanka a titi hukuncin zaman Gidan Gyaran Hali na shekara 1, ko biyan tarar Naira 80,000.
Freedom Radio ta rawaito cewa kotun ta kuma umarci Tsulangen ya biya Hukumar tace Fina-finai Naira 20,000 ladan wahalar da ta yi.
A ƙarshe, kotun ta ja hankalin Umar din da ya zama matashi na gari, domin ya kyautata gobensa.