HomeSashen HausaWest Ham Za Ta Siyar Da Mohammed Kudus Don Ɗauko Ademola Lookman

West Ham Za Ta Siyar Da Mohammed Kudus Don Ɗauko Ademola Lookman

-

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta West Ham United da ke buga gasar Premier League a Ingila na shirin siyar da ɗan wasanta Mohammed Kudus domin samun damar ɗauko ɗan wasan gaba na Najeriya, Ademola Lookman.

Rahotanni daga kafafen wasanni na Ingila na nuna cewa West Ham tana duba yiwuwar rabuwa da Kudus, wanda ƙungiyar ta sayo daga Ajax ta ƙasar Netherlands a bara, domin ƙarfafa ɓangaren gaba da Ademola Lookman, wanda ke taka rawar gani a Atalanta ta Italiya.

Lookman yayi fice a kakar da ta gabata, musamman bayan da ya jefa ƙwallaye uku (hat-trick) a gasar Europa League da ta tabbatar wa Atalanta samun kambun zakara. Wannan bajinta na daga cikin ababen da suka jawo hankalin West Ham da wasu manyan ƙungiyoyi a Turai.

Idan har West Ham ta cimma matsaya da Atalanta da kuma wakilan Lookman, to akwai yiyuwar ganin ɗan wasan na Najeriya ya koma London kafin kakar 2025/2026 ta fara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‘Yan Tsagin Wike Sun Gindaya Wa PDP Sabbin Sharudda Kafin Babban Taro

Wasu ƴaƴan jam'iyyar PDP da ake ganin ƴan tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike ne sun gudanar da wani taro a daren jiya Litinin a Abuja,...

Ƴansanda Sun Kama Mutane Biyu Dake Safarar Manyan Makamai Daga Jihar Jigawa Zuwa Katsina

Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina ta yi nasarar chafke masu safarar Makamai daga jihar Jigawa zuwa ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina, inda aka kama su...

Most Popular