HomeSashen HausaRasuwar Buhari Baƙar Lahadi Ce Ga Najeriya- Inji Kashim Shettima

Rasuwar Buhari Baƙar Lahadi Ce Ga Najeriya- Inji Kashim Shettima

-

Mataimakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana matukar kaɗuwarsa da rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana ranar rasuwarsa a matsayin bakar rana ga Najeriya

A cikin sakon ta’aziyyar da ya aike wa manema labarai a ranar Lahadi, Shettima ya ce Najeriya ta rasa kataɓus sakamako babbar asarar da ta tafka na rashin tsohon shugaban Muhammadu Buhari

“Zuciyata ta cika da alhini da jimami, yayin da al’ummar kasar ke zaman makokin daya daga cikin manyan shugabannin da ba kasafai zamani ke iya samar da su ba irin mai girma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR,” in ji Shettima.

Mataimakin shugaban kasar wanda a kwanakin baya ya ziyarci Buhari a wani asibiti a kasar Birtaniya, ya ce ya sa ran tsohon shugaban kasar zai sami sauki cikin gaggawa ya dawo gida. Inda yake cewa “Wannan rashi ya yi muni matuka fiye da yadda baki zai iya bayyanawa, labarin mutuwar ya zo min a daidai lokacin da nake masa tsammanin murmurewa cikin sauri bayan da na ziyarce shi a asibiti a Burtaniya,” in ji shi.

Mataimakin shugaban kasar ya mika ta’aziyya ga iyalan Buhari, da gwamnati da al’ummar jihar Katsina, da gwamnatin Najeriya da ‘yan Najeriya. Inda yayi musu fatan samin dangana da fatan ƙasar za ta rike kyawawan koyarwar marigayi Buhari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

NATA Mourns Former President Buhari, Describes Him as a Pillar of National Service

NATA Mourns Former President Buhari, Describes Him as a Pillar of National Service Nigeria Automobile Technicians Association (NATA) Katsina State Council Mourns the Passing of Former...

Katsina NUJ Mourns Former President Muhammadu Buhari, Describes His Death as Monumental Loss

The Katsina State Council of the Nigeria Union of Journalists (NUJ) has expressed deep sorrow over the death of Nigeria’s former President, Muhammadu Buhari, GCFR,...

Most Popular