HomeSashen HausaNafi Son Cigaban Ƙasa A Kan Kowanne Muradi Na Kaina- Inji Sule...

Nafi Son Cigaban Ƙasa A Kan Kowanne Muradi Na Kaina- Inji Sule Lamido

-

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya bayyana cewa a shirye yake ya goyi bayan kowanne irin tsarin siyasa da zai kawo tsaro da zaman lafiya a Najeriya, musamman ma kafin zaɓen 2027. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025, Lamido ya nuna cewa babban burinsa shi ne haɗin kan ƙasa da kwanciyar hankali, ba wai cika muradinsa na siyasa kawai ba.

Ya ce, duk da cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, bai hana shi yin aiki tare da wasu ƙungiyoyi ko shugabannin siyasa da nufin taimaka wa ƙasar idan hakan zai amfani Najeriya baki ɗaya.
Lamido ya ƙaryata maganganun da aka yaɗawa na cewa yana shirin barin PDP musamman zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), inda ya tabbatar da cewa biyayyarsa ga PDP na nan.

Amma ya shaida cewa yana ganin akwai bukatar ‘yan siyasa su yi haɗin kai duk da bambancin jam’iyya domin magance matsaloli kamar rashin tsaro, yunwa, da rikice-rikicen cikin gida. Ya ce, “Ko da na zauna a PDP, ƙofa abuɗe take ga duk wata hanya da za ta tabbatar da tsaron Najeriya, zaman lafiyar tare da cigaba.”

Har ila yau, ya gargadi cewa kawai ƙirƙirar sabbin jihohi ko canza iyakoki wanda hakan ba zai warware matsalolin ƙasar nan na dindindin ba.

Dangane da ziyarar siyasa da aka yi kwanan nan, musamman haɗuwar Sanata Kwankwaso da Shugaba Tinubu, Lamido ya bayyana cewa kowanne ɗan siyasa na da ‘yancin yanke irin wannan shawarar kuma babu laifi a yin hakan.

Ya ƙara da cewa ‘yan siyasa yana da kyau su fifita amfanin ƙasa sama da rigingimu na jam’iyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Hukumar NSCDC A Katsina Ta Yi Sabon Shugaba

Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Katsina ta samu sabon kwamanda bayan sauyin shugabanci da ya gudana a ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, 2025.   A...

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Horas Da Malamai 250 Da Faransifal 50, Don Inganta Ilmin Jihar

Ma’aikatar Ilimi a Matakin Farko da na Sakandire a jihar Katsina, haɗin gwiwa da Majalisar Turai (British Council), ta ƙaddamar da wani muhimmin shirin horaswa...

Most Popular