Rahoton da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta fitar ya bayyana cewa komishinan sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya karɓi cin hancin dala $30,000 daga wani shahararren dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, domin tsaya masa a matsayin mai ceto (surety).
Namadi, wanda aka taɓa bayyana a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a 2013 bisa zargin zamba, ya samu nadin komishina a gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ne bayan zaben 2023.
Wata majiya daga hedikwatar SSS ta ƙasa ta shaida wa Daily Nigerian cewa sun gudanar da bincike cikin sirri game da lamarin kuma sun ba da shawarar a tsige Namadi daga mukaminsa.
Bayan zazzafar suka daga jama’a, Gwamna Abba Yusuf ya kafa kwamitin bincike don zakulo gaskiyar lamarin cikin mako guda.
Majiyoyi sun ce gwamnan ya fusata sosai da rawar da komishinan ya taka, duba da irin matakan da gwamnati ke dauka wajen yaki da fataucin kwayoyi a Kano.
Wani rahoto ya bayyana cewa Mr. Namadi na fama da rikice-rikice da shugaban kungiyar NURTW, Kabiru Labour, kan kudin haraji na Naira dubu 500 da yake tilasta wa kungiyar kowanne wata.
Bugu da ƙari, ana zargin cewa komishinan yana gudanar da harkokin ma’aikatarsa ba tare da hadin kan sakataren dindindin, Abdulmumin Babani ba – wanda hakan ke janyo tsaiko da rashin amincewa da takardun memo fiye da 30 daga ma’aikatar.
Wani daga cikin misalan hakan shi ne batun siyan tricycles na hasken rana (solar) wanda aka gabatar gaban majalisar zartarwa ba tare da shigar da Ma’aikatar Sufuri ba.
Da aka tuntubi Mr. Namadi don jin ta bakinsa, ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa: “Ban san wani abu daga cikin zarge-zargen da kuka lissafa ba, ba gaskiya ba ne.”
Sai dai bayan ƴan mintoci kadan da wannan tattaunawa ta wakilin DAILY NIGERIAN da Namadi, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya kira dan jaridar yana zargin sa da cin zarafin abokin aikinsa.