Monday, June 29, 2026
HomeLabarai‎'Yan Najeriya Biyu Sun Mutu a Yaƙin Ukraine

‎’Yan Najeriya Biyu Sun Mutu a Yaƙin Ukraine

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan Najeriya biyu – Hamzat Kazeem Kolawale da Mbah Stephen Udoka – sun rasu a ƙasar Ukraine yayin da suke fafatawa a matsayin sojojin haya a ɓangaren Russia.

‎Majiyoyi sun ce mutanen biyu sun shiga aikin sojan haya ne a lokacin da ake cigaba da yaƙi tsakanin kasashen biyu. An ce sun mutu ne a fagen daga, sai dai ba a fitar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ba.

Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga mahukuntan Najeriya kan lamarin, yayin da iyalai da abokan arziki ke jimamin rasuwarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments