Makarantar koyar da Wasan Kwallon kafa ta Katsina Football Academy ta Taya Yan Wasan ta biyar (5) murnar samun girma zuwa Babbar Kungiyar Kwallon kafa ta Katsina United.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan wasanni na Makarantar Shamsuddeen Ibrahim ya fitar biyo bayan da Babbar Kungiyar Kwallon kafar ta katsina United ta fitar da jerin sunayen Yan Wasa Yan asalin Jihar Katsina da ta dauka ga bannin fara Gasar Kakar Wasanni ta NPFL zango na 2025/2026.
Sanarwar ta ambato Daraktan kwalejin yana bayyana daukar Yan Wasan Makarantar ta katsina football academy amatsayin wata nasara a rayuwar su ta Kwallon kafa, inda ya bukace su dasu kasan ce jakadu na gari a yayin da suke a Babbar Kungiyar Kwallon kafar ta Jiha.
Da ya ke yima Yan Wasan fatan alkhairi, Shamsuddeen Ibrahim ya Kuma Yi Kira garesu dasu kara zage damtsi, su Kuma Yi aiki tukuru a yayin da zasu tun Kari Babbar Gasar Kwallon kafa ta Kasar Nigeria.
Yan Wasan da suka samu nasarar shiga Kungiyar Kwallon kafar ta katsina United sun hada da Usman Abdullahi, Ahmad Nasir, Umar Yusuf, Abubakar Hassan da Kuma Kabir Muhammad Kabir.