Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), reshen jihar Katsina, ta tabbatar da cafke wani Matashi mai shekaru 18 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a yankin Sabuwar Unguwa, ƙaramar hukumar Katsina.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun hukumar, SC Buhari Hamisu, ya fitar a madadin Kwamandan Jihar, Aminu Datti Ahmad, ya jaddada cewa an kama wanda ake zargin, Hamza Ahmad, ne a ranar Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025, ta hanyar sintiri na musamman da rundunar ta ƙaddamar a yankin.
Kwamandan Ahmad ya bayyana cewa, wannan nasara ta biyo bayan sabbin dabaru da aka ɗauka na yaƙi da aikata laifuka da safarar miyagun kwayoyi a jihar. Ya ce miyagun ƙwayoyi na barazana ga lafiyar al’umma da ci gaban tattalin arziki, don haka rundunar ba za ta lamunci irin wannan dabi’a ba.
Kamar yadda Nigerian Post ta bibiyi rahoton, ya jaddada cewa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma bincike na ci gaba da gudana a kan lamarin, Rundunar ta kuma tabbatar da cewa, za ta ci gaba da Jajircewa don kawo ƙarshen ayyukan bata-gari, masu lalata tattalin arziki da sauran miyagu a Katsina
Kwamandan ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da haɗin kai ta hanyar samar da ingantattun bayanai cikin lokaci, yana mai gode wa al’umma kan irin goyon bayan da suke bayarwa ga hukumomin tsaro.