HomeSashen HausaGwamnatin Jihar Katsina Ta Horas Da Malamai 250 Da Faransifal 50, Don...

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Horas Da Malamai 250 Da Faransifal 50, Don Inganta Ilmin Jihar

-

Ma’aikatar Ilimi a Matakin Farko da na Sakandire a jihar Katsina, haɗin gwiwa da Majalisar Turai (British Council), ta ƙaddamar da wani muhimmin shirin horaswa ga Malamai da shugabannin makarantun Sakandire a jihar.

Taron gudana ranar Talata, 23 ga watan Satumba 2025, a babban ɗakin taro na KCK da ke cikin birnin Katsina.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Kwamishiniyar ilimi a Matakin Farko da na sakandare ta jihar Katsina, Hajiya Zainab Musa Musawa, ita ce ta jagoranci taron horas wa ga malaman na jihar Katsina.

Da take jawabi a wajen taron, Hajiya Zainab Musa Musawa ta jaddada cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar ilimi a matsayin ginshiƙi na cigaban al’umma, kuma wannan shiri zai taimaka wajen inganta ayyukan Malamai da ɗalibai a jihar.

Kwamishinar ta ce shirin ya tanadi horaswa ga Malamai 250 da kuma shugabannin makarantun sakandiri 50, ƙarƙashin Shirin Ƙarfafa Harshen Turanci na Malamai wato Strengthening Teachers English Proficiency (STEP) da na koyar da shugabanci wato Instructional Leadership Programmes.

A cewar Kwamishiniyar, manufofin yin wannan taron horaswar shi ne domin inganta ƙwarewar malamai a ɓangaren harshen turanci, da tsara dabarun koyarwa ga shugabannin makarantu.

Ta yi ƙarin haske da cewa, da yawan malaman da aka horas za su Ƙarfafa harshen Turanci a Aji da kuma gabatar da dabarun Koyarwa.

Inda ta ƙara jaddada cewa, wannan horaswa na ɗaya daga cikin manyan matakan da gwamnatin jihar Katsina ke ɗauka domin tabbatar da ingantaccen ilimi a faɗin jihar.

Taron ya samu halartar jami’an Gwamnati, wakilai daga Majalisar Turai (British Council), shugabannin makarantu, da Malamai daga sassa daban-daban na jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Hukumar NSCDC A Katsina Ta Yi Sabon Shugaba

Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Katsina ta samu sabon kwamanda bayan sauyin shugabanci da ya gudana a ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, 2025.   A...

Ma’aikatar Shari’a Ta Katsina Ta Naɗa Mace Ta Farko A Matsayin Babbar Magatakarda

Ma'aikatar Shari’a ta jihar Katsina ta naɗa Basira Umar a matsayin mace ta farko da za ta rike mukamin Babbar Magatakarda ta Babbar Kotun Katsina...

Most Popular