HomeSashen HausaRikicin Boko Haram Ya Fi Yadda Ake Zato Rikitarwa- Inji Goodluck Jonathan...

Rikicin Boko Haram Ya Fi Yadda Ake Zato Rikitarwa- Inji Goodluck Jonathan Tsohon

-

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce rikicin Boko Haram ya fi rikice-rikicen da Najeriya ta taɓa fuskanta rikitarwa, yana mai bayyana cewa a wani lokaci mayakan ƙungiyar sun mallaki makamai fiye da sojojin ƙasa.

Jonathan ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin ƙaddamar da littafin tsohon babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) mai suna “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” a turance.

Ya ce rikicin Boko Haram ya sha bamban da na ‘yan tawayen Niger Delta saboda alaƙarsa da ƙasashen waje da akidar tsattsauran ra’ayi da kuma makaman zamani.

Tsohon shugaban ƙasar ya tuna cewa sace ɗaliban Chibok a 2014 ya kasance ɗaya daga cikin manyan raunuka da ba za a taɓa mantawa da su ba.

Jonathan ya jaddada cewa ba za a iya ɗaukar Boko Haram kawai a matsayin matsalar tsaro ba, yana mai kiran a haɗa ayyukan tsaro da kyakkyawar gwamnati, rage talauci, ƙarfafa matasa da tabbatar da adalci domin samun zaman lafiya na dindindin.

Taron ya samu halartar tsofaffin shugabanni da manyan jami’an tsaro, ministoci, da sarakunan gargajiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Hadiza Gabon Na Shirin Barin Kaduna Zuwa Kano Da Shirin Talk Show

Daya daga cikin makusantar tsohuwar Jarumar Kanywood Hadiza Gabon, ya tabbatar wa Jaridar ALFIJIR NEWS, wanda a yanzu jarumar ta fara tinanin dauke zauren Shirin...

Sojoji Sun Ceto Mutune 7 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Tsanyawa, Jihar Kano

Sojojin Operation MESA da suka haɗa da jami’an Birgediya ta 3 ta rundunar sojin Najeriya, sojojin saman Najeriya da kuma ’yansanda sun ceto mutune bakwai...

Most Popular