Wasu majiyoyi na kusa da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan, sun shaida wa jaridar Punch cewa tsohon shugaban na duba yiwuwar sake komawa fagen siyasa ta hanyar shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Bisa ga rahoton, wannan batu na daga cikin tattaunawa da ake yi a cikin gida da wajen jam’iyyar, wanda idan ya tabbata, zai iya jawo sabon salo a harkokin siyasar Najeriya, musamman a fagen zabe mai zuwa.
Kamar yadda Nigerian Post ta samu daga DCL Hausa, tun bayan barinsa mulki a 2015, Jonathan ya kasance cikin manyan mutanen da ake mutuntawa a siyasar Najeriya da ma duniya baki ɗaya, kasancewarsa mai shiga tsakani a rigingimun kasa da kasa.
Sai dai har yanzu ofishin Jonathan bai fitar da wata sanarwa kai tsaye ba kan wannan jita-jita, lamarin da ya sa jama’a ke ci gaba da tattaunawa a kafafen sada zumunta, wasu na ganin zai kawo karfin gwiwa ga ADC, yayin da wasu kuma ke kallon hakan a matsayin sabon kalubale ga manyan jam’iyyun da ke rike da madafun iko.
Idan aka tabbatar da hakan, masu sharhi na cewa siyasar Najeriya za ta sake shiga wani sabon salo da ba a zata ba.