Hukumar Rijistar Kamfanoni ta Ƙasa (CAC) ta sanar da cewa ta soke rijistar Ƙungiyar Matasan Nijeriya (NYCN), sakamakon rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar ƙungiyar.
Wannan mataki ya fito ne daga wasiƙar da CAC ta aikewa Ma’aikatar Ci gaban Matasa a ranar 6 ga watan Oktoba, 2025, inda aka bayyana cewa rikicin cikin gida ya saɓa wa tanade-tanaden dokar CAMA, lamarin da ya wajabta ɗaukar tsauraran matakai.
Domin kaucewa gibi a shugabanci, CAC ta kafa Kwamitin Gudanarwa na Wucin Gadi (IMC) da zai riƙe jagorancin ƙungiyar na tsawon shekara guda, daga ranar da aka sanar da matakin.
Sai dai, shugaban NYCN, Amb. Sukubo Sara-Igbe Sukubo, ya yi watsi da wannan hukunci, yana mai cewa:
“CAC ta ɗauki wannan mataki ne ba bisa tsarin ƙungiyar ba, kuma ba mu amince da shi ba.”
A gefe guda, wasu kungiyoyin matasa sun yi maraba da matakin, suna cewa zai taimaka wajen tsaftace shugabancin NYCN da dawo da martabar ta, yayin da wasu suka yi gargadi cewa hakan na iya barin matasan ƙasar ba tare da wata ingantacciyar ƙungiya da ke wakiltarsu ba.
Masu sharhi na ganin cewa wannan matakin na CAC na iya zama hanya ta dawo da gaskiya da tsari a harkokin ƙungiyoyin matasa, amma babban abin tambayar anan shine:
Shin sabon kwamitin zai iya shawo kan rikicin da ya daɗe yana addabar ƙungiyar, ko kuwa zai ƙara rarrabuwar kawuna a tsakanin matasan Nijeriya?