Hukumar Tsaro da Civil Defence ta Ƙasa (NSCDC), reshen Jihar Katsina, ta bayyana aniyarta na ƙarfafa haɗin gwiwa da Rundunar Sojin Sama da kuma Ma’aikatar Shari’a ta jihar, domin ƙara tabbatar da tsaro da kare rayukan al-umma.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, SC Buhari Hamisu, ya fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Oktoba 2025, inda Sanarwar ta ce sabon kwamandan NSCDC a Katsina, Kwamandan AD Moriki, ya kai ziyarar bangirma ga Kwamandan 213 na Rundunar Sojin Sama, Air Commodore GI Jibia, wanda kuma shi ke shugabantar rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma.
Haka kuma, kwamandan ya ziyarci ofishin Kwamishinar Shari’a kuma Lauyan Gwamnatin Jihar Katsina, Hajiya Fadila Mohammed Dikko, a sakatariyar jihar da ke kan hanyar Kano.
A jawabinsa, Comdt Moriki ya jaddada kudurin Janaral Komandan NSCDC, Farfesa Ahmed Abubakar Audi (mni, OFR), na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da kare muhimman kayayyakin gwamnati a duk faɗin ƙasar. Ya bayyana cewa ziyarar ta kasance ta ƙarin sani, neman fahimtar juna da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa.
A nasu bangaren, Kwamandan Sojin Sama da kuma Kwamishinar Shari’a sun yi maraba da sabon kwamandan tare da jaddada kyakkyawar dangantaka da ke tsakaninsu da NSCDC, inda suka tabbatar da ci gaba da haɗin kai.
Sanarwar ta ce fitattun abubuwan da suka biyo bayan ziyarar sun haɗa da musayar kyaututtukan tunawa da kuma ɗaukar hotunan haɗin gwiwa.