Tsare-tsare 3 Da Sojojin Amurka Ke Yi Kan Tunkarar Najeriya– Rahoton NY Times
Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar sojin ƙasar ta gabatar wa shugaba Trump tsare- tsaren yadda za a kai wa Najeriya hari, bayan umarnin da shugaban ya ba wa shalkwatar tsaron ƙasar ta Pentagon bayan zargin ana kisan Kiristoci Najeriyar.
Jaridar New York Times ta bayyana cewa tsare-tsaren su ƙushi zaɓi uku na yadda sojojin MAurkan za su iya shiga Najeriya da suka haɗa da:
Gagarumin hari, wanda zai ƙunshi aika wata rundunar mayaƙan ruwa ta musamman zuwa gaɓar tekun Guinea tare da rakiyar manyan jiragen sama na yaƙi, waɗanda za su iya yin ɓarin wuta kan ƴanbindiga a yankin arewacin Najeriya.
Matsakaicin hari, wanda zai kunshi aika jirage marasa matuƙa, domin tattara bayanan sirri da ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin masu tayar da ƙayar baya, da ayarinsu da ababen hawansu.
Sassauƙan hari, wanda zai fi mayar da hankali ga batun samar da bayanan sirri, da bayar da taimakon kayan aiki, da kuma gudanar da sintirin haɗin gwiwa da dakarun Najeriya domin ganin an kakkaɓe ƴan ƙungiyar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, kamar yadda jaridar ta wallafa.
Wannan dai na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurkar Donald Trump, ya yi na kai hari Najeriyar saboda zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi.
