Wani matashin jami’in Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, Lt. A.M. Yarima, wanda ya yi rashin jituwa kwanan nan da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya kubuta daga yunkurin kisan gilla da aka yi masa da yammacin Lahadi.
Majiyoyin soja sun shaida wa Vanguard cewa wasu mutane da ba a san ko su waye ba, sanye da baƙaƙen kaya, suna cikin manyan motoci biyu kirar Hilux marasa lambar rajista, sun bi sawun Yarima. Ana zargin motocin sun bi shi daga tashar mai ta NIPCO da ke kusa da Line Expressway zuwa Gado Nasco Way.
A cewar majiyar, jami’in ya lura ana bin sawunsa, sai ya aiwatar da wata dabara ta dabarun tsaro, inda ya samu ya tsere wa waɗanda ake zargin ‘yan harin ne. Lamarin ya faru ne kimanin ƙarfe 6:30 na yamma.
Majiyar ta ƙara da cewa ana bincike kan lamarin, kuma ana daukar shi da muhimmanci yadda ya dace, tare da ƙarin bayanai da aka ɓoye domin kada a kawo cikas ga binciken.
