Fargaba da tashin hankali sun mamaye al’ummar Maga, cikin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, bayan wasu ’yan bindiga sun afka Government Girls Comprehensive Senior Secondary School a daren jiya Lahadi suka yi garkuwa da dalibai mata 25, tare da kashe Malam Hassan Makuku, mataimakin shugaban makarantar, yayin da yake ƙoƙarin kare ɗalibansa.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa rundunar ta fara bincike domin ceto daliban cikin koshin lafiya.
Rahotannin kafaafen watsa labarai sun nuna cewa maharan sun yi ta’addancin ne ba tare da wata turjiya ba, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin tashin hankali da jimami, musamman ganin yadda harin ya yi sanadin rasa rayuwar malamin makarantar.
A halin da ake ciki, Gwamna Idris Nasir ya tura mataimakinsa, Sanata Umar Tafida, zuwa makarantar domin gudanar da cikakken bincike da kuma jajanta wa iyalai da al’ummar da abin ya shafa.
Jama’a da dama dai, na ci gaba da ƙalubalantar yawaitar hare-haren a yankuna daban-daban na arewacin ƙasar, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro na ganin sun ƙara ninka matakan kariya domin kare rayuka da dukiyoyi, musamman ma a makarantun gwamnati.
