Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar IPOB da aka haramta, an yanke masa hukuncin daurin rai da rai bayan kotu ta same shi da laifin ta’addanci.
Alƙalin da ya yanke hukuncin, Justice James Omotosho, ya bayyana hukuncin ne a ranar Alhamis.
An yanke wa Kanu hukuncin daurin rai da rai a kan tuhuma ta 4, 5 da 6 cikin tuhume-tuhume bakwai da ake masa, yayin da aka yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari kan tuhuma ta biyu.
