HomeSashen Hausa‎Gobara Ta Tashi A Ofishin Hukumar Karbar Haraji A Abuja

‎Gobara Ta Tashi A Ofishin Hukumar Karbar Haraji A Abuja

-

Wata gobara ta tashi a ɗaya daga cikin ofisoshin Hukumar Karɓar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da ke birnin tarayya Abuja, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a tare da jawo firgici a yankin Wuse Zone 5.

‎Gobarar, wadda ta tashi a ranar Asabar, ta kama ne a bene na huɗu na ginin ofishin hukumar da ke Lamba 15, Sokode Crescent, inda bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta suka nuna yadda wutar ke cin wasu sassan ginin, yayin da hayaki ya turnuke sama

‎A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar FIRS, Sikiru Akinola, ya fitar, hukumar ta bayyana cewa jami’an tsaro da ke bakin aiki sun ɗauki matakin gaggawa tun da wutar ta fara, kafin isowar jami’an kashe gobara.

‎Sanarwar ta ce, “Da taimakon Hukumar Kashe Gobara ta Babban Birnin Tarayya (FCT Fire Service) da sauran jami’an agajin gaggawa, an samu nasarar shawo kan gobarar cikin lokaci tare da hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan ginin.”

‎Hukumar FIRS ta tabbatar da cewa babu asarar rai da aka samu, ko da yake wasu sassan ofishin sun samu ɓarna. Haka kuma, an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar, inda ake zargin matsalar lantarki na daga cikin abubuwan da ake kyautata zaton ya jawo gobarar.

‎Lamarin dai ya jawo hankalin ma’aikata da mazauna yankin, inda da dama suka yaba wa gaggawar da jami’an tsaro da na kashe gobara suka nuna wajen daƙile wutar, abin da ya taimaka wajen hana tafka babbar asara.

‎Hukumar ta ce za ta ƙara ɗaukar matakan tsaro da na kariya daga gobara a ofisoshinta domin kauce wa faruwar irin wannan lamari nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ƙasar Mali Ta Ƙirƙiri Sabuwar Rundunar Soji Ta Musamman

Ƙasar Mali, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Mulkin Soji, Kanal Assimi Goïta, ta ƙaddamar da wata sabuwar rundunar soji ta musamman mai suna Rapid Intervention Battalion (RIB). ‎ ‎Manufar...

POCACOV: Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina Ta Kara Zage Dama Wajen Yaki da Laifuka

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Bello Shehu, MNIM, ta shirya wani Maci na wayar da kan jama’anta kan Yaki...

Most Popular