HomeSashen HausaƘasar Mali Ta Ƙirƙiri Sabuwar Rundunar Soji Ta Musamman

Ƙasar Mali Ta Ƙirƙiri Sabuwar Rundunar Soji Ta Musamman

-

Ƙasar Mali, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Mulkin Soji, Kanal Assimi Goïta, ta ƙaddamar da wata sabuwar rundunar soji ta musamman mai suna Rapid Intervention Battalion (RIB).

‎Manufar kafa wannan runduna ita ce ƙarfafa ƙarfin aiki da ingancin rundunar Sojojin Mali (FAMa), tare da inganta saurin mayar da martani ga duk wani nau’in barazanar tsaro a fadin kasar.

‎Sabuwar rundunar za ta kasance mai saurin motsi da tsauraran horo, domin tinkarar hare-haren ‘yan ta’adda, rikice-rikicen cikin gida da kuma kare ikon ƙasa da lafiyar al’umma.

‎Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Mali ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro, musamman a yankunan arewa da tsakiyar kasar, inda gwamnati ke ƙoƙarin ƙarfafa ikon ta da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

DA ƊUMI-ƊUMINSA: ‘Yanbindiga Sun Sako Sauran Ɗalibai 115 Da Aka Sace a Makarantar St. Mary’s, Niger

‎‘Yanbindiga sun sako rukunin ƙarshe na ɗalibai 115 da aka sace daga St. Mary’s Catholic Private Primary and Secondary School da ke ƙauyen Papiri, a...

‎Gobara Ta Tashi A Ofishin Hukumar Karbar Haraji A Abuja

Wata gobara ta tashi a ɗaya daga cikin ofisoshin Hukumar Karɓar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da ke birnin tarayya Abuja, lamarin da ya tayar da...

Most Popular