A wani mataki na musamman domin tabbatar da isasshen tsaro, Kwamandan NSCDC na Jihar Katsina, AD Moriki, ANIM, ya amince da tura jami’ai 1,256 domin tabbatar da zaman lafiya da kuma kare Muhimman Kadarorin Ƙasa da Ababen More Rayuwa, ya tura su ne kafin lokacin bukukuwan Kirsimeti da bayan bukukuwan Kirsimeti da kuma sabuwar shekara.
Kwamandan ya bayyana hakan ne yayin fitar da Umarnin Aiki a ranar Litinin, 22 ga Disamba, 2025, a Hedikwatar NSCDC ta Jihar Katsina. A wata gajeriyar ganawa da manyan shugabannin gudanarwa, Kwamandan ya jaddada cewa, sabbin dabarun aiki da aka sake sabuntawa kamar tsauraran sa ido, tattara bayanan sirri, hulɗa da al’umma da haɗin gwiwa na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Haka kuma, Commanda Moriki ya umurci dukkan shugabannin sassa da rukuni, kwamandojin yankuna, jami’an rassa, kwamandojin rukuni da rundunonin musamman da su tabbatar da cikakken haɗin kai da ingantaccen sintiri domin samar da tsaro mai ƙarfi a faɗin jihar. Ya kuma yi kira ga dukkan jami’an da aka tura da su kasance masu ladabi, jajircewa, ƙwarewa da kuma yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da bukukuwa ba tare da wata tangarɗa ba.
Umarnin aikin ya bayyana cewa, an tura jami’ai zuwa wurare kamar coci-coci, wuraren shakatawa da taruka, tashoshin mota, kasuwanni, wuraren bukukuwa, da sauran muhimman wurare na Gwamnatin Tarayya, Jiha da Kananan Hukumomi. Haka kuma, an tura jami’an sirri zuwa wurare masu matuƙar muhimmanci domin samar da bayanan sirri cikin lokaci da za su taimaka wajen dakile ayyukan bata-gari a jihar.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar Manema Labarai da jami’im hulda da Jama’a na rundunar SC Buhari Hamisu, ya fitar.
Kwamandan ya yi kira ga jama’a da su ƙara sa ido tare da kai rahoton duk wani motsi ko abu da ake zargi zuwa ofishin NSCDC mafi kusa. Ya kuma taya dukkan mabiya addinin Kirista murna tare da yi musu fatan Barka da Kirsimeti da sabuwar shekara mai albarka tun tuni.
