HomeSashen Hausa‎Yarjejeniyar Haraji Najeriya da Faransa Ta Haifar da Ruɗani

‎Yarjejeniyar Haraji Najeriya da Faransa Ta Haifar da Ruɗani

-

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tabbatar da sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna (MoU) tsakanin Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) da Hukumar Haraji ta Faransa (DGFiP), matakin da ke nufin inganta tsarin haraji ta hanyar fasahar zamani da musayar ƙwarewa.

‎A cewar FIRS, yarjejeniyar ta mayar da hankali ne kan tsarin haraji ta hanyar fahasar zamani (digitalization), horar da ma’aikata, da musayar fahimta a fannin haraji, musamman wajen fuskantar ƙalubalen harajin ƙetare da inganta ayyukan tattara kuɗaɗe.

‎Sai dai matakin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jam’iyyu da ƙungiyoyin farar hula, inda wasu ke nuna damuwa kan yiwuwar tsaron bayanai da ikon tattalin arzikin ƙasa. Wasu ƙungiyoyi sun yi kira da a bayyana cikakken abin da yarjejeniyar ta ƙunsa, suna mai cewa jama’a na da haƙƙin sanin irin wadannan muhimman shirin.

‎Da take maida martani, FIRS ta jaddada cewa ba a bai wa Faransa ikon sarrafa bayanan haraji na Najeriya ba, kuma ba a buɗe ƙofar shiga bayanan masu biyan haraji ba. Hukumar ta ce yarjejeniyar shawara da haɗin gwiwa ce kawai, wadda ke ƙarƙashin dokoki da ƙa’idojin kariyar bayanai ta Najeriya.

‎Masana harkokin tattalin arziki na ganin cewa irin wannan haɗin gwiwa na iya taimakawa wajen ƙara inganci da gaskiya a tsarin haraji, amma sun ce buƙatar bayyana gaskiya da saka idon Majalisar Ƙasa na da muhimmanci domin kwantar da hankalin jama’a.

‎Yayin da gwamnati ke ganin yarjejeniyar a matsayin wata dama ta gyaran tsari, muhawarar da ta biyo baya na nuna irin ƙalubalen da ke tattare da haɗin gwiwar ƙasashen waje a muhimman sassan tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

NSCDC Ta Tura Jami’ai 1,256 A Jihar Katsina, Don Kare Muhimman Kadarorin Kasa Da Ababen More Rayuwa

A wani mataki na musamman domin tabbatar da isasshen tsaro, Kwamandan NSCDC na Jihar Katsina, AD Moriki, ANIM, ya amince da tura jami’ai 1,256 domin...

‎‘Yansanda Sun Jaddada Ƙara Matakan Tsaro Yayin Bukukuwan Kirsimeti

‎Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin shiga bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya ba da...

Most Popular