HomeLabarai‎Gwamnan Gombe Ya Kori Wasu hadimansa Huɗu Kan Zargin Cin Zarafin Kansila

‎Gwamnan Gombe Ya Kori Wasu hadimansa Huɗu Kan Zargin Cin Zarafin Kansila

-

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kori wasu hadimansa huɗu daga aiki nan take, bayan an same su da laifin cin zarafin wani kansila mai ci, Abdulrahman Abubakar Sharif, mai wakiltar yankin Shamaki a ƙaramar hukumar Gombe.

‎Matakin ya biyo bayan rahoton kwamitin bincike da bayanan jami’an tsaro, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana.

‎Waɗanda aka kora sun haɗa da Adamu Abdullahi Danko, Garba Mohammed Mai Rago, Rabiu Suleman Abubakar da Alhaji Ibrahim Baban Kaya, dukkaninsu Mataimaka ne na Musamman (SAS II) a fannoni daban-daban.

‎Gwamnatin jihar ta umurce su da su miƙa dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsu nan take.

‎A sanarwar da Babban Daraktan Yaɗa Labarai, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamnatin ta jaddada cewa ba za ta lamunci cin zarafi ba, tare da ci gaba da kare doka, adalci da zaman lafiya a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Nigeria Edge Iran 2–1 in International Friendly

The Nigeria national football team, the Super Eagles, defeated Iran 2–1 in a friendly match played on Friday. The match took place at the Mardan Sport...

Brazil Doesn’t Necessarily Have to Win the World Cup –Vinícius

Renowned Brazilian footballer Vinícius Júnior stated that his country does not necessarily have to be among the teams that win the 2026 FIFA World Cup. He...

Most Popular