HomeSashen HausaKatsina Za Ta Karɓi Baƙuncin Mauludin Ƙasa na Inyass karo na Uku...

Katsina Za Ta Karɓi Baƙuncin Mauludin Ƙasa na Inyass karo na Uku a Janairu 2026

-

An bukaci Gidan Rediyon Jihar Katsina da ya bayar da cikakken hadin kai da goyon baya wajen watsa dukkan ayyukan Mauludin Ƙasa na Inyass na bana da za a gudanar a jihar.

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Mauludin Ƙasa na Inyass, Shariff Abba Bashir ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin zuwa ziyarar girmamawa ga shugabancin Gidan Rediyon Jihar Katsina,Malam Lawal Attahiru Bakori.

Kamar yadda ya ce, manufar ziyarar ita ce neman ƙarfafa haɗin gwiwa da gidan rediyon, domin samun yaɗa labarai da cikakken ɗaukar taron maulidin a faɗin jihar.

Shugaban kwamitin ya kuma bayyana cewa Jihar Katsina ce ke karɓar bakuncin taron karo na uku, wanda aka tsara zai gudana a ranar Asabar, 17 ga watan Janairun shekarar 2026.

Ya bayyana Gidan Rediyon Jihar Katsina a matsayin gidan rediyo mai faɗin isar da saƙo, wanda ke yaɗa bayanai, yana ilmantarwa tare da wayar da kan al’umma kan harkokin addini.

Shariff Abba Bashir ya yi kira ga masu hannu da shuni a jihar da su bayar da gudummawar dukiyoyinsu domin samun nasarar gudanar da taron.

A nasa jawabin, Janar Manajan Gidan Rediyon na Jihar Katsina, Malam Lawal Attahiru Bakori, ya yi alƙawarin ba da cikakken gudunmawa wajen watsa dukkan ayyukan Mauludin na Ƙasa na Inyass da ke tafe.

Malam Lawal Attahiru Bakori ya nuna jin daɗinsa da godiya kan ziyarar, inda ya tabbatar wa mambobin kwamitin cewa gidan rediyon na kowa da kowa ne, kuma a ko da yaushe a shirye yake ya haɗa kai da ƙungiyoyin addini domin yaɗa harkokin addini a faɗin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Jirgin Marar Matuƙi Ya Faɗo a Dajin Kontagora, Jihar Neja

Wani jirgin marar matuƙi (drone) ya faɗo a wani daji da ke kusa da garin Kontagora, a Jihar Neja, da yammacin yau Juma'a, kamar yadda...

Manufar Kwankwaso Ita Ce Haddasa Rikicin Siyasa Da Bautar da Jama’ar Jihar Kano Kan Siyasa- Kano Youth Democratic Agenda

Kungiyar matasan da ke fafutikar dorewar mulkin dimokraɗiyya da shugabanci nagari a jihar Kano ta yi Allah wadai da manufar Kwankwaso wajen son haddasa rikicin...

Most Popular