HomeSashen HausaManufar Kwankwaso Ita Ce Haddasa Rikicin Siyasa Da Bautar da Jama'ar Jihar...

Manufar Kwankwaso Ita Ce Haddasa Rikicin Siyasa Da Bautar da Jama’ar Jihar Kano Kan Siyasa- Kano Youth Democratic Agenda

-

Kungiyar matasan da ke fafutikar dorewar mulkin dimokraÉ—iyya da shugabanci nagari a jihar Kano ta yi Allah wadai da manufar Kwankwaso wajen son haddasa rikicin siyasa da hargitsa zaman lafiya a jihar Kano

 

A cewar, shugaban kungiyar Kwamarad Bashir Sharada ya ce basu yi mamakin ricikin da ya dabaibaye jam’iyyar NNPP da kuma rashin jituwar da ke faruwa tsakanin Kwankwaso da Abba domin batu ne na nuna isa da iko wanda Tsohon Gwamnan jihar Sen. Rabi’u Kwankwaso ya dade yana nuna katsalandan kan harkokin gwamnatin jihar Kano.

 

Ya ci gaba da cewa tuntuni sun san haka za ta faru, domin batu ne kawai na lokaci kuma ga shi Kwankwaso ya fara nuna son zuciyarsa kan batun katsalandan game da sha’anin Tafiyar da harkokin gwamnati a jihar Kano.

 

A wata sanarwa da kungiyar ta (KYDA) suka fitar ga manema labarai sun bayyana Kwankwaso a matsayin gajimare mai son kawo rudani da nuna kakagida duk mutumin da ya Gwamna jihar Kano inda buÆ™atarsa ce kawai abin kallo bata al’ummar jihar ba.

 

Kwamarad Bashir, ya ce ba bu abun da yafi yin tasiri kan rikicin Kwankwaso da Abba game da kaomawa APC sai karbe ikon Tafiyar gwamnati na yadda hatta hade-haden mukami shi ne yake aiwatar hannu kawai Abba ke saka wa.

 

Haka kuma kungiyar ta ce ya kamata hankalin al’umma ya dawo tare dasu domin ko rikicin Kwankwaso da Ganduje batu na neman karbe ikon jiha da yunkuri bautar da Æ´a’yan talakawa ta hanyar amfani da su kan rikice-rikicen siyasa da harkar daba. Domin babu yadda za ace Kwankwaso ya bata da Abba da Ganduje ace kuma shi ke da gaskiya don ba zai yiyyuba.

 

Tunda farko shugaban kungiyar Kwamarad Bashir, ya ce tuni suka yi bincike suka gano cewa matasan da Kwankwaso ke turawa kasar waje da sunan karatu duk bigece domin gwamnonin da suka gaje shi Ganduje da Abba ya bari da biyan bashi.

 

Kungiyar ta ce Kwankwaso ya cika tsantsagwaron son rai da son zuciya, da kuma rashin haÆ™uri. ”Duba da yake yake wadaka da kudaden harajin da ake karba a jihar Kano” Inji kungiyar

 

Kwamarad Bashir ya kara da cewa dama Hausawa kan ce Æ™arya fure kawai take ba ta ‘Æ´a’Æ´a, don haka ga shi lokacin da ake jira ya zo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Za Ta Karɓi Baƙuncin Mauludin Ƙasa na Inyass karo na Uku a Janairu 2026

An bukaci Gidan Rediyon Jihar Katsina da ya bayar da cikakken hadin kai da goyon baya wajen watsa dukkan ayyukan Mauludin Ƙasa na Inyass na...

‎Jirgin Marar Matuƙi Ya Faɗo a Dajin Kontagora, Jihar Neja

Wani jirgin marar matuƙi (drone) ya faɗo a wani daji da ke kusa da garin Kontagora, a Jihar Neja, da yammacin yau Juma'a, kamar yadda...

Most Popular