Wasu bayanai sun fito kan dalilin da ya sa aka ɗage shirin sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, duk da an riga an kammala shirye-shiryen farko.
A ranar Juma’a, jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa gwamnan ya kammala tanadin sanar da sauya sheƙarsa a Ranar Litinin mai zuwa. Sai dai kafin aiwatar da shirin, aka samu sauyin jadawali Wanda ya haifar da ɗagewar matakin.
Rahotanni sun nuna cewa hedkwatar APC ta ƙasa ta riga ta shirya Gwamnan zai kasance mutum na farko da za a yi wa rajista a Kano a sabon tsarin rajistar jam’iyyar na yanar gizo. Bisa wannan tsari, tsohon Gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ne zai raka Gwamna Abba Yusuf zuwa mazabarsa ta Diso Ward domin yin rajista a manhajar jam’iyyar tare da karɓar katin membobinsa.
Bayan kammala rajistar gwamnan, shi ma Gwamna Abba Yusuf zai raka Ganduje zuwa Garinsa na Dawakin Tofa Domin sabunta rajistarsa a sabon tsarin jam’iyyar.
Sai dai duk da waɗannan shirye-shirye, Wasu dalilai na ciki sun sanya aka ɗage aiwatar da sauya sheƙar, lamarin da ya haifar da jinkiri a sanarwar da ake sa ran yi.
