HomeSashen HausaGwamnatin Gombe Ta Bai Wa Iyalan ’Yanjarida 7 Da Suka Rasu Tallafin...

Gwamnatin Gombe Ta Bai Wa Iyalan ’Yanjarida 7 Da Suka Rasu Tallafin Miliyan 14

-

Gwamnatin Jihar Gombe ta raba naira miliyan 14 ga iyalan ’yan jarida bakwai da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a kan hanyar Billiri zuwa Kumo.

 

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya mika naira miliyan biyu ga kowanne iyali a matsayin tallafin kuɗi domin taimakawa wajen jana’iza da sauran buƙatu.

 

Njodi ya ce tallafin na daga cikin ƙudurin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na rage raɗaɗin rashi ga iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta ɗauki alhakin biyan kuɗaɗen jinya na ’yan jaridar da suka jikkata.

 

Ya kuma bayyana alhini kan asarar da ta rutsa da jihar da kuma harkar aikin jarida, yana mai jaddada cewa kuɗin ba diyya ba ne.

 

A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Alhassan Yahaya Abdullahi, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta aiwatar da inshorar rayuwa da lafiya ga ’yan jarida.

 

Da yake magana a madadin iyalan mamatan, Lauya Abubakar Ahmed ya yaba wa gwamnan, yana mai cewa tallafin zai taimaka matuƙa wajen biyan buƙatun gaggawa da na dogon lokaci na iyalan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Katsina Judiciary Trains Magistrates on ICT, AI and New Media

The Katsina State Judiciary on Tuesday organised a specialised capacity-building workshop for magistrates aimed at strengthening the justice system in the digital age. ‎The workshop, themed...

Alƙalin Alƙalai na Jihar Katsina Ya Ƙaddamar Da Bada Horo Ga Alƙalai Kan Ilimin (AI) da Kafofin Yaɗa Labarai Na Zamani

Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Katsina ta shirya wani taron horaswa na musamman ga alƙalan majistire, domin ƙarfafa tsarin shari’a daidai da buƙatun zamani. Taron wanda...

Most Popular