Tsofaffin Kansiloli, sun rushe shugabancin ƙungiyar tsofaffin Kansilolin ta ƙasa reshen jihar Katsina, inda suka zaɓi Hon. Dauda Kurfi, a matsayin shugaban ƙungiyar tsofaffin Kansiloli a jihar.
Tunda farko dai, Tsofaffin kansilolin, sun sanar da kafa sabuwar ƙungiya ta haɗin kai da nufin rushe duk wata tsohuwar ƙungiya da ke rarraba su, domin su rika magana da murya ɗaya tare da ƙarfafa zumunci da walwala a tsakaninsu.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar, a wani taron Manema Labarai da aka gudanar 7 ga watan Janairu 2026, biyo bayan amincewar dukkan shugabannin tsofaffin kansiloli daga matakai daban-daban.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, a yayin zantawa da Manema Labarai shugabannin da suka goyi bayan ƙudurin sun haɗa da Hon. Usman Rimaye, wanda ya jagoranci tsofaffin Kansiloli tun na zangon shekarar 1999; sai Hon. Ibrahim Suleiman Daura; Hon. Halilu Maje; da Hon. Yusuf Iro Dutsinma, shugaban ƙungiyar Kansilolin na shekarar 2011.
A sakamakon amincewar da aka cimmawa, Alhaji Dauda Ahmad Kurfi, ya zama shugaban sabuwar ƙungiyar, bi sa yardar sauran jagororin ƙungiyoyin tsofaffin Kansiloli.
Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Alhaji Dauda Kurfi, ya bayyana cewa, ƙungiyar ta kuduri aniyar samar da walwala ga tsofaffin kansilolin Jihar Katsina, da samar da yanayi mai kyau na fahimta da haɗin kai a faɗin ƙananan hukumomin jihar.
Ya ce, manufarsu ita ce su haɗa kan su gaba ɗaya, su daina rarrabuwar kai, su kuma gina ƙungiya mai ƙarfi da za ta wakilci muradun tsofaffin kansiloli yadda ya kamata.
Haka kuma, sabuwar ƙungiyar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, tare da alƙawarin marawa gwamnatin sa baya domin ci gaba da ganin alherin da take kawowa al’umma, da kuma tallafa wa dukkan manufofin sa da suka shafi ci gaban jihar.
Jerin shugabannin ƙungiyar sun haɗa da;
1. Hon. Dauda Kurfi – Chairman
2. Hon. lbrahim Suleiman Daura – Secretary
3. Hon. Usman Rabe Rimaye – Deputy Chairman
4. Hon. Yusuf lbrahim (Castro) – V/Chairman Katsina Zone
5. Hon. Sani Aliyu Jarkuka – V/Chairman Daura Zone
6. Hon. lbrahim Kasko Kankara – VIChairman Funtua Zone
7. Hon. Armaya’u Dauda Gozaki – Treasurer
8. Hon. Usman A. Usman Na’alma – Youth Leader
9. Hon. Kabir Umar Ajiwa – Financial Secretary
10. Hon. Yusuf Laila Katsina – Organizing Secretary
11. Hon. Aminu Adamu Albasu – Auditor
12. Hon. Nura Musa Radda – Legal Adviser
13. Hon. Abubakar Muh’d Mainasara – Assit. Secretary
14. Hon. Yusuf Adamu Kurfeji – Assit. Treasurer
15. Hon. Sa’idu Lawal Funtua – Assit. Organizing Secretary
16. Hon. Nasiru Muhammad lbrahim – Assit. Financial Sec.
17. Hon. Halilu lsyaku Maje – P.R.OI
18. Hon. Abdulmutallab Rabe – P.R.O. II
