Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da naɗin sabbin manyan sakatarorin jihar.
Gwamnan ya ce an gudanar da naɗin bi sa cancanta da sabbin manyan sakatarorin da aka naɗa suka nuna ta hanyar cin jarabawar da Cibiyar Ma’aikata ta Najeriya ta gudanar a madadin gwamnatin jihar Katsina.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Mallam Falalu Bawale, ya buƙaci waɗanda aka naɗan da su yi aiki da ƙwarewa tare da nuna ƙwazo.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, sabbin manyan sakatarorin sun haɗa da Tukur Hassan Dan Ali, Junaidu Muntari da Yahaya Abdullahi.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na shugaban ma’aikatan jihar Abubakar Yaro Bindawa ya fitar.
