Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara jefa sabuwar barazana ga Gwamnatin Najeriya, yana cewa zai ɗauki matakai masu tsauri ciki har da yuwuwar amfani da karfin soja, idan har ba a dakatar da kashe kashen da ake zargin ana yi wa Kiristoci a ƙasar ba.
Wannan ya zo ne bayan rahotannin da ya bayyana a matsayin tsanantawar addini da zarge zargen rashin isasshen mataki daga gwamnatin Abuja.
Trump ya bayyana cewa Amurka za ta iya dakatar da taimakon ƙasa da ƙasa ga Najeriya idan ba a yi gaggawar kawo ƙarshen harin da ake yiwa al’ummomin Kirista ba, tare da umartar ma’aikatan tsaro na Amurka su shirya yiwuwar aiki a Najeriya domin kare waɗannan al’ummomi.
Gwamnatin Najeriya ta musanta cewa akwai wani shiri na kisan kiristoci na banbanci, tana mai cewa tattalin rashin tsaro ya shafi duka addinai da yankuna a ƙasar, kuma tana aiki tare da jami’an tsaro wajen dakile matsalar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce wannan ba zai hana ƙasar cigaba da kare dukkan ‘yan ƙasa ba.
Wannan matsayi ya haifar da tattaunawar diflomasiyya tsakanin gwamnatin Najeriya da Amurka domin samo mafita ta hanyoyin tsaro da fadada haɗin gwiwa kan yaki da ta’addanci.
