HomeSashen HausaYaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

-

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe mai gidansa, Abdul’aziz Aliyu Dan Malam, ta hanyar caka masa almakashi.

‎Majiyar Reality TV news ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne da yammacin Asabar, 17 ga watan Janairu, 2026, da misalin karfe 5:40 na yamma, a lokacin da marigayin ya kulle shagonsa bayan kammala harkokin kasuwanci, yana kan hanyarsa ta komawa gida tare da mahaifiyarsa.

‎Bayanai daga majiyoyi na kusa da iyalan marigayin sun ce an samu cacar baki ne tsakanin marigayin da wasu daga cikin yaran shagon, sakamakon zargin sata, lamarin da daga bisani ya rikide zuwa tashin hankali. A dalilin rikicin ne, daya daga cikin yaran shagon ya caka masa almakashi a gaban mahaifiyarsa.
‎Inda aka garzaya da marigayin zuwa Asibitin Koyarwa ta Tarayya (FTH) Gombe, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa.

‎Rahotanni sun kuma nuna cewa marigayin sabon ango ne, kasancewar an daura aurensa ne a 26 ga watan Disamba, 2025, makonni uku kacal kafin faruwar wannan lamari.

‎An dai shirya gudanar da sallar jana’izar marigayin da misalin karfe 11 na safiyar Lahadin yau a Masallacin Juma’a na Bolari, dake birnin Gombe.

‎Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan matakin da aka dauka ba, yayin da jama’a ke ci gaba da fatan ganin an gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎An Cafke Wani Mutum Da Zargin Sayar Da Jaririn ‘Yar’ uwarsa Naira Miliyan 2 a Legas

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 30 da haihuwa bisa zargin sayar da jaririn ‘yar uwarsa mai wata daya kacal...

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun damƙa matashiya Walida Abdullahi Ibrahim ga Gwamnan Jihar Jigawa,...

Most Popular