Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ake zargin cewa tana yin watsi da sojojin da suka jikkata yayin aiki.
Shelkwatar tsaron ta bayyana cewa, sabanin wani bidiyo da ya yaɗu wanda ke zargin “rashin kulawa da halin ko-in-kula ga walwalar sojojin da suka jikkata a bakin aiki,” walwalar jami’anta, musamman waɗanda suka samu raunuka yayin aiki, na daga cikin manyan abubuwan da take ba muhimmanci.
A cewar wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar ranar Talata, dukkan sojojin da suka jikkata a yayin ayyuka ko fagen fama suna da haƙƙin samun cikakken kulawar lafiya, a cikin gida ko a ƙasashen waje, gwargwadon nau’i da tsananin raunukan da suka samu, bisa ƙa’idojin kiwon lafiya da sojojin Najeriya suka tanada.
Sanarwar ta ce: ”Sojojin Najeriya na ba da damar samun kulawa ta musamman ga waɗanda suka jikkata sosai a wuraren kiwon lafiya ko a ƙasashen waje idan irin wannan kulawar ta zama wajibi.”
