Tuesday, June 16, 2026
HomeLabarai‎Shelkwatar Tsaro Ta Musanta Yin Watsi Da Sojojin Da Suka Jikkata a...

‎Shelkwatar Tsaro Ta Musanta Yin Watsi Da Sojojin Da Suka Jikkata a Fagen-daga ‎

Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ake zargin cewa tana yin watsi da sojojin da suka jikkata yayin aiki.

‎Shelkwatar tsaron ta bayyana cewa, sabanin wani bidiyo da ya yaɗu wanda ke zargin “rashin kulawa da halin ko-in-kula ga walwalar sojojin da suka jikkata a bakin aiki,” walwalar jami’anta, musamman waɗanda suka samu raunuka yayin aiki, na daga cikin manyan abubuwan da take ba muhimmanci.

‎A cewar wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar ranar Talata, dukkan sojojin da suka jikkata a yayin ayyuka ko fagen fama suna da haƙƙin samun cikakken kulawar lafiya, a cikin gida ko a ƙasashen waje, gwargwadon nau’i da tsananin raunukan da suka samu, bisa ƙa’idojin kiwon lafiya da sojojin Najeriya suka tanada.

‎Sanarwar ta ce: ‎”Sojojin Najeriya na ba da damar samun kulawa ta musamman ga waɗanda suka jikkata sosai a wuraren kiwon lafiya ko a ƙasashen waje idan irin wannan kulawar ta zama wajibi.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments