Shigar Abba APC Yanzu Zan Yi Bacci Da Ido Biyu– Inji Barau
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Kano da su bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf cikakken goyon baya tun gabanin sauya shekarsa zuwa jam’iyyar.
Sanata Barau ya ce Shugaban ƙasar ya jaddada muhimmancin haɗin kai da haɗin gwiwa domin samun ingantaccen shugabanci a jihar.
Barau ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a Kano, a ranar Talata.
Ya ce Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin gogaggen shugaba a harkar siyasa, ya shawarci masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da su yi aiki kafada da kafada da gwamnan, tare da gujewa duk wani aiki da zai iya karkatar da hankalinsa daga samar da nagartaccen shugabanci ga al’ummar Jihar Kano.
“Yau rana ce da zan kwanta cikin natsuwa saboda jam’iyyarmu ta samu gwamna. Fiye da shekara guda, muna karɓar ‘yan sauya sheka daga jam’iyyu daban-daban, ciki har da NNPP. Yanzu, da yardar Allah, mun karɓi gwamna mai ci na jiha kamar Kano,” in ji Barau.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya ce yanzu APC a Kano ya kamata ta mai da hankali wajen tallafawa Gwamna Yusuf don ya yi nasara, inda ya lura cewa haɗin kai a cikin jam’iyyar yana da matuƙar muhimmanci don cimma ci gaba.
“Abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne tallafa masa da kuma ba shi shawara, har da addu’a. Halin da ake ciki a Kano na bukatar mu hada kai ta hanyar dimokuradiyya don taimaka masa ya yi nasara,” in ji shi.
Barau ya bayyana cewa, bayan shigar gwamnan cikin APC, duk wani nau’i na fafatawa ta siyasa da burin ƙashin kai a cikin jam’iyyar ya kamata a ajiye a gefe don tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaba.
