HomeSashen HausaYa Kamata Sojoji Su Ba ’Yan Najeriya Haƙuri Kan Musanta Yunƙurin Juyin...

Ya Kamata Sojoji Su Ba ’Yan Najeriya Haƙuri Kan Musanta Yunƙurin Juyin Mulki– Falana

-

Femi Falana, babban lauya mai kare haƙƙin ɗan ada, ya ce rundunar sojin Najeriya ta ruɗi jama’a ta hanyar musanta zargin yunƙurin juyin mulki a baya, yana mai cewa ya dace su ba ’yan Najeriya haƙuri.

 

Falana ya bayyana hakan ne bayan da hedikwatar tsaro ta tabbatar cewa akwai shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tare da sanar da cewa za a gurfanar da wasu jami’an soji a gaban kwamitocin shari’a na soji.

 

A watan Oktoban 2025 ne gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin ranar ’yancin kai, lamarin da daga baya aka danganta da zargin yunƙurin juyin mulki, duk da cewa hedikwatar tsaro ta musanta hakan a wancan lokaci.

 

Da yake magana a shirin Sunrise Daily na Channels Television, Falana ya ce sabon bayani daga sojoji na nuna cewa an yaudari ’yan Najeriya, don haka ya zama wajibi a nemi afuwa.

 

Ya kuma ce bai dace a gurfanar da jami’an da aka tsare a kotun soja ba, domin zargin ya kai matsayin cin amanar ƙasa, wanda kotun tarayya ko ta jiha kaɗai ke da hurumin sauraro.

 

Falana ya ƙara da cewa jami’an da aka tsare suna da haƙƙin samun lauyoyi da ’yan uwansu, yana mai kira ga hukumomi su saki duk waɗanda ba a gurfanar da su a hukumance ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

An Kama Tsohon Abokin Ganduje Yayin Da Yake Shirin Barin Kano

Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano sun kama wani muhimmin mutum da ake zargi da badakalar mallakar Dala Inland Dry Port—wani shiri na biliyoyin nairori—a...

Ba Da Jimawa Ba Za Mu Kawo Ƙarshen Rikicin Masarautar Kano– Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce nan ba jimawa ba za ta kawo karshen rikicin da ya daɗe yana faruwa kan masarautar Kano, inda mutum biyu...

Most Popular