Tuesday, June 16, 2026
HomeLabaraiGwamnan Kano Da Muƙarrabansa Za Su Yi Nadamar Barinmu Nan Gaba– Inji...

Gwamnan Kano Da Muƙarrabansa Za Su Yi Nadamar Barinmu Nan Gaba– Inji Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da muƙarrabansa za su yi nadamar barin jam’iyyar a nan gaba.

Kwankwaso ya ce ficewar gwamnan daga NNPP ta bai wa mutane da dama mamaki, har wasu da kan su suna ganin ya yi babban butulci.

“Mutane da dama sun ɗauka wata yarjejeniya ce aka ƙulla tsakanina da shi, ko tsakaninsa da wasu. A wasu lokuta na kan kasa yarda da yadda abubuwa ke tafiya,” in ji Kwankwaso.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments