Shugaban rundunar horaswa ta Sojin Sama ta Nijeriya, Air Vice Marshal Esen Paul Efanga, ya kai ziyara sansanin Sojin Sama na Kainji domin duba
shirye-shiryen aiki da ƙarfinsu wajen yaƙi da ƴan ta’adda a sassan ƙasar nan.
A yayin ziyarar, Efanga ya yabawa jami’ai bisa ƙwazo da jajircewa, tare da nuna gamsuwa da yadda jiragen sama ke gudanar da ayyukansu yadda ya dace.
Ya jaddada cewa Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya na ci gaba da samun rinjaye a sararin samaniya, tare da cikakken shiri na kai farmaki a kowane lokaci.
Shugaban rundunar ya kuma tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa Sojin Sama na da cikakken iko da ƙarfin kare martabar ƙasa, inda ya ce ba za a sassauta ba wajen ci gaba da kai hare-hare cikin ƙarfi da daidaito har sai an samu tsaro mai ɗorewa
