HomeLabaraiNSCDC a Katsina, Ta Kama Wata Mace Bisa Zargin Cin Zarafin Yarinya...

NSCDC a Katsina, Ta Kama Wata Mace Bisa Zargin Cin Zarafin Yarinya Ƙarama a Mashi

-

Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), reshen Jihar Katsina, ta cafke wata mace bisa zargin cin zarafi da dukan wata yarinya a garin Mashi da ke Karamar Hukumar Mashi.

 

Kamar yadda Nigerian Post ta bibiyi Rahotan, wannan na kunshe ne a cikin sanarwar manema labarai da SC Buhari Hamisu, Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, ya sanya wa hannu. Sanarwar ta ce cafken ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da hukumar ta samu, inda Kwamandan NSCDC na Jihar Katsina, CC AD Moriki, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi.

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, an cafke Hauwa’u Gwaska, mai shekaru 37, ‘yar Unguwar Gabas a Mashi, bisa zargin cin zarafin yarinya mai suna Azima Abubakar, wadda take karkashin kulawarta kuma ‘yar’uwar mahaifinta. Ana zargin ta da yi wa yarinyar duka sau da dama.

 

A yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin, tana mai cewa fushi ne ya jawo mata aikata hakan. Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da ita a gaban kotu bisa tanadin doka.

 

NSCDC ta bukaci iyaye da masu kula da yara da su rika yin taka-tsantsan wajen daukar matakan tarbiyya, tare da kaucewa duk wani abu da zai iya cutar da yara. Haka kuma, rundunar ta yabawa al’umma bisa hadin kai, tare da rokon su, da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin karfafa tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

CAF Strips Senegal of AFCON 2025 Title, Awards It to Morocco

The Confederation of African Football (CAF) has stripped Senegal of the 2025 Africa Cup of Nations (AFCON) title and awarded it to Morocco. In a statement...

Mutane 23 Sun Mutu, Sama da 100 Sun Jikkata a Harin Bama-bamai a Maiduguri

‎Aƙalla mutane 23 sun mutu, yayin da mutane 108 suka jikkata sakamakon wasu jerin fashewar bama-bamai da suka auku a daren Litinin. ‎ ‎Rundunar ’yan sandan Jihar...

Most Popular