Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta miƙa mata da yara 46 da aka yi safararsu daga Jihar Katsina, bayan da aka kama su yayin da suke ƙoƙarin bin hanyoyin da ba su dace ba zuwa Jamhuriyar Chadi.
An kama mutanen ne a kan iyakar Maiduguri a Jihar Borno, inda ake zargin suna kan hanyarsu ta fita ƙasashen waje domin neman rayuwa mai inganci, kafin daga bisani a dawo da su Katsina a ranar Juma’a.
Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa da aka tattauna da su, ciki har da Naja’atu ASalisu, uwa ga yara biyu daga Ƙaramar Hukumar Zango, ta ce matsin tattalin arziƙi da burin samun halal ne suka tilasta musu tafiyar.
Ta ce: “Mun tashi ne domin zuwa N”Jummaina Chadi, amma jami’an shige da fice suka kama mu suka dawo da mu. Tun farko burinmu shi ne mu nemi kuɗi ta hanyar halal, ta hanyar kasuwanci.”
Naja’atu ta bayyana cewa tana sana’ar dinki, kuma ta tara kuɗin tafiyar ne da taimakon mahaifinta.
Ta ƙara da cewa: “Ina da aure da yara biyu masu shekaru huɗu da biyu. Na bar su a gida ne domin neman hanyar samun abin rayuwa. Yanzu muna neman tallafin kuɗi domin fara ƙaramar sana’a mu samu mu zauna lafiya.”
Wata daga cikin waɗanda abin ya shafa, Maryam Alhaji Salis daga Ƙaramar Hukumar Zango, ta ce ta shirya tafiya Chadi ne domin samun kuɗin da za ta yi amfani da su kafin aurenta.
Ta ce: “Ina shirin yin aure, amma ba ni da kayan daki, shi ne dalilin tafiyata.”
Maryam ta bayyana cewa ta aro wani ɓangare na kuɗin mota, sannan ta sayar da ragowar dabbobinta domin ɗaukar nauyin tafiyar.
Ta ce: “Ko da yake kayan daki ba dole ba ne kafin aure, amma yana da kyau mutum ya mallake su. Idan Allah Ya ba ni nasara, zan dawo gida.”
Haka kuma, wata uwa ga yara takwas, Ladidi Audu, ta bayyana cewa rashin lafiya da rasa hanyar samun abin rayuwa ne suka sa ta yanke shawarar tafiya ƙasashen waje.
Ta ce: “Babban dalilin da ya sa na so barin ƙasar shi ne rashin lafiyata. Ba ni da aiki, kuma ina fama da matsanancin rashin lafiya.”
Ladidi ta ba da labarin yadda ta rasa sana’arta bayan ta ji munanan ƙone-ƙone yayin soyayyen akara, inda ta shafe watanni ana yi mata jinya.
Ta ƙara da cewa: “An gaya mini cewa ana taimakon talakawa da marasa lafiya a can, shi ya sa na amince na tafi.”
