HomeSashen HausaHisba Ta Bayyana Wuraren Da Ta Haramta Ƙwallon Ƙafa Lokacin Ramadan a...

Hisba Ta Bayyana Wuraren Da Ta Haramta Ƙwallon Ƙafa Lokacin Ramadan a Katsina

-

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ba ta haramta wasan ƙwallo gaba ɗaya a watan Ramadan ba, sai dai ta ɗauki matakin hana yin wasan da daddare a kan tituna da kuma wuraren da ke haddasa cunkoso da kawo cikas ga zirga-zirga.

‎Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Sashen Fasahar Sadarwa na Hisbah a Dandume, Malam Bin Haris, ya fitar domin fayyace matsayar hukumar ga al’umma.

‎A cewar sanarwar, an takaita wasan ƙwallo da daddare ne musamman a wuraren da ke kawo tangarda ga zirga-zirgar ababen hawa, da kuma a lokutan da jama’a ke tafiya masallatai domin gudanar da ibadu a watan Ramadan. Hukumar ta ce matakin na da nufin kare lafiyar al’umma, tabbatar da tsaro, da samar da kwanciyar hankali a wannan wata mai alfarma.

‎Haka kuma, hukumar ta yi kira ga al’umma da su guji yaɗa jita-jita ko karkatar da bayani dangane da umarninta, tare da bin doka, mutunta hanyoyi, da kuma bada haɗin kai ga jami’an tsaro domin samun zaman lafiya da nutsuwa a duk tsawon watan Ramadan.

‎Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta jaddada cewa ƙoƙarinta na ci gaba da kasancewa ne wajen gyara al’umma da kare martabar addini ba tare da tauye hakkokin jama’a ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Court Orders INEC to Register National Democratic Party

A Federal High Court sitting in Abuja has ordered the Independent National Electoral Commission (INEC) to register the National Democratic Party (NDP) as a political...

Idan Tinubu Bai Janye Maganar Haraji Ba Zai Gani A Akwatin Zaɓensa– Sheikh Yakubu Musa Katsina

Sheikh Yakubu Musa Katsina ya bayyana takaicin sa akan irin yadda musamman 'yan arewa suka kasa cim amfanin gwamnatin shugaba Bola Tinubu. A cewar shehin malamin...

Most Popular