Wata tawagar masana kimiyya ta samu nasarar gano ƙasusuwan wani nau’in dinosaur da ya ɓace a yankin hamadar Sahara da ke cikin Jamhuriyar Nijar. Masanan sun bayyana cewa wannan halitta na daga cikin jinsin Spinosaurus mirabilis, wadda ta rayu kusan shekaru miliyan 95 da suka gabata.
Masu binciken sun ce wannan ganowa na daga cikin manyan nasarori a fannin ilimin tarihi da kimiyyar halittu, domin ta taimaka wajen ƙara fahimtar yadda manyan dabbobin da suka ɓace suka rayu a Afirka a zamanin da.
Rahotan Tashar Geo News ya nuna cewa Spinosaurus mirabilis dabba ce mai girma wadda ke rayuwa a kusa da ruwa, tana cin kifaye, kuma yanayin ƙasusuwan da aka gano ya nuna cewa yankin Sahara a wancan lokaci yana da ruwa da ciyayi.
Masana sun jaddada cewa wannan bincike zai buɗe sabbin ƙofofi na bincike tare da jawo hankalin duniya kan muhimman kayan tarihi da ke ƙasashen Afirka.
