HomeLabaraiAn Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi

-

An Damƙa Walida Ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Namadi Ɗanmoɗi

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun damƙa matashiya Walida Abdullahi Ibrahim ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Danmodi a daren Jiya a hedikwatar Hukumar dake Abuja.

Gwamnan ya samu rakiyar Shugaban majalisar dokokin Jihar da Kwamishinan shari’a da Kwamishiniyar lamuran Mata. Ana sa ran Gwamnatin jihar za ta Kula da Walidan.

In ba a manta ba dai taƙaddama ta dabaibaye batun matashiyar mai suna Walida Abdullahi, bayan iyalanta sun zargi wani jami’in DSS mai suna Ifeanyi Onyewuenyi da sace ta daga gidansu tare da tsare ta na tsawon lokaci ba tare da sanin inda take ba.

Rahotanni sun ce ana zargin jami’in ya sauya Mata addini daga Musulunci zuwa Kiristanci tare da canza mata suna zuwa Chinaza, lamarin da iyalanta suka ce an yi ba tare da yardarta ba ko kuma amincewar danginta kamar yadda jaridar Daily Trust da Aminiya suka wallafa Labarin.

Haka kuma, bayan shafe lokaci mai tsawo a hannunsa, an ce Walida ta haifi jaririya mace, abin da ya kara jawo cece-kuce da damuwa a tsakanin iyalanta da kuma al’umma, musamman dangane da zargin take mata ’yanci da kuma amfani da iko ba bisa ka’ida ba.

Lamarin ya jawo kira daga kungiyoyi da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam da su ke bukatar gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiya, tare da tabbatar da adalci ga Walida da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi idan har zarge-zargen sun tabbata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Albaba Announces Return Bid for Katsina Assembly Seat

Hon. Aliyu Albaba has declared his intention to contest for a seat in the Katsina State House of Assembly to represent Katsina Local Government Area...

Kurfi APC Stakeholders Rally for Unity, Pledge Support for Party Success

Key stakeholders of the APC in Kurfi Local Government Area have held a special meeting aimed at strengthening unity and fostering cohesion among party members...

Most Popular